Da duminsa: Jami'an tsaron jihar Kebbi sun harbe da dama tareda bindige daya cikin yan bindiga da suka farmaki karamar hukumar Augie (Hotuna)


A ci gaba da kokarin kawar da jihar Kebbi daga dukkan laifuka, rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta samu labarin cewa, a ranar 21 ga watan Agusta, 2022, da misalin karfe 3 na dare, ‘yan bindiga da dama sun mamaye kauyen Tiggi da ke karamar hukumar Augie. Yankin Jihar Kebbi.

Hakan na kunshe ne a wata takarda da Kakakin rundunar yansandan jihar Kebbi SP Nafi'u Abubakar ya raba wa manema labarai a garin Birnin kebbi ranar Lahadi wanda shafin labarai na isyaku.com ya gani.

Takardar ta ce bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sandan da aka tura yankin tare da hadin gwiwar sojoji da ’yan banga, sun yi artabu da ‘yan bindigar. Sakamakon haka, an kashe daya daga cikin ‘yan bindigar kuma da dama sun tsere da raunukan bindiga. Sai dai kuma an kwato bindiga kirar AK 47 guda daya.

Da yake yabawa kwazon da tawagar ‘yan sanda da sojoji da ‘yan banga suka yi wajen kai farmaki kan ‘yan ta’addan, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, CP Ahmed Magaji Kontagora ya nanata cewa a shirye rundunar take wajen jajircewarta don ganin ta tabbatar da tsaro ga. al’umma tare da yaki da ayyukan ‘yan fashi da yan bindiga a jihar Kebbi gaba daya.

Hakazalika, CP Ahmed Magaji Kontagora ya kara yin kira ga al’ummar jihar Kebbi na gari da su ci gaba da bayar da hadin kai ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da nufin rage yawan laifuka a jihar.Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN