FG za ta siya wa kasar Nijar motocin N1.4b, Minista ta yi karin haske



Gwamnatin tarayya, a ranar Laraba, ta kare kudurin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kashe Naira biliyan 1.145 ga Jamhuriyar Nijar, Daily Trust ta ruwaito.

Ministar Kudi, Kasafin da Tsare-Tsare ta Kasa Zainab Ahmed, ta yi wannan tsokaci ne a lokacin da ta ke gabatar da tambayoyi bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja.

Ministar, wacce ta ce shugaban kasar na da ‘yancin yanke shawara don amfanin Najeriya, ta kara da cewa "wannan ba shi ne karon farko da kasar ke ba da irin wannan gudunmawa ga makwabtanta ba."

Ta ce shugaban kasar na da hurumin daukar irin wadannan shawarwari bayan ya yi nazari a tsanake.

A cewarta, gwamnatin Najeriya ta sha ba da irin wannan tallafi ga kasashe kamar su Kamaru, Nijar da ma Chadi, Vanguard ta ruwaito.

A fadinta:

“Shugaban kasar ya yi nazarin abubuwan da ake bukata bisa bukatar shugabanninsu. An amince da irin wadannan bukatun kuma ana ba da gundunmawar.

“An yi hakan ne don inganta karfinsu na kare kasashensu, kamar yadda ya shafi tsaro da kuma Najeriya."

Ta kara da cewa:

“Yan Najeriya na da ‘yancin yin tambayoyi, amma kuma shugaban kasa shi ma yana da alhakin tantance abin da zai amfani kasar nan, kuma ni kaina ba zan iya kalubalantar hukuncin ba.

“Na fada wannan ba shi ne karon farko ba kuma Najeriya a matsayin kasa ta ba da taimako ga makwabtanmu. Yin haka shi ne mafi alheri ga Najeriya.”

Wani rahoto a baya ya nuna cewa shugaba Buhari ya amince da ba da motoci kirar Toyota Land Cruiser kusan guda 10 ga ‘yan jamhuriyar Nijar, amma bai bayyana dalilin yin hakan ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN