Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi dan shekara 27 mai suna Mato Yohannah da laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 3 a karamar hukumar Ganjuwa da ke jihar.
Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Mohammed Wakil, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 30 ga watan Agusta, 2022.
"A ranar 24 ga watan Agustan 2022 da misalin karfe 11 na safe, wani Mato Yohannah 'm' mai shekaru 27 a kauyen Jimbin, karamar hukumar Ganjuwa jami'an tsaro na hedikwatar Ganjuwa sun kama shi bayan ya yi lalata da wata (sara Ezra), ba ainihin sunanta bane 'f' mai shekaru 3yrs . na kauyen Jimbin, karamar hukumar Ganjuwa," in ji PPRO.
“A binciken da ake yi, wanda ake zargin ya amsa laifin yi wa kananan yara fyade a karo na biyu, haka kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin gurfanar da shi gaban kuliya".