Wadannan yan mata Maryam da Hadiza sun fito daga kauyukan kewayen garin Birnin kebbi ne a jihar Kebbi. Suna sana'ar sayar da dafaffen ganye kamar Rama da sauransu. Kafar labarai na isyaku.com ya tattaro.
Wani abin sha'awa shine yadda yan matan ke iya hada fiye da N2500 a rana daya. A cewarsu sukan fito talla daga karfe 10 na safe har zuwa karfe 5 ko 6 na yamma.
Idan ka hada jimilar kudin da suke samu a cikin kwana 30, adadin ya isa ya zama madogaran kawar da talauci a rayuwarsu.
Ko daidai ne matasa su tsaya jiran sai Gwamnati ta basu aiki bayan sun kamma karatu?