Mazauna gari sun kama wata karamar yarinya inda suka lakada mata duka bisa zarginta da sace janareta a garin Warri dake jihar Delta.
A cewar Warri Aproko, lamarin ya faru ne a titin Lori- Igba, kusa da titin Deco a daren Lahadi, 3 ga watan Yuli.
Daya daga cikin Yan matan biyu ta tsere sai dai ita kuma dayan ta fada hannun fusatattun matasa da suka lakaɗa mata duka.
Asirinsu ya tonu ne bayan sun yi nassarar sace janareton suka sa a cikin wata Keke Napep kuma suka yi kokarin tserewa daga Unguwar kafin dubunsu ta cika.
Rubuta ra ayin ka