Rashin tsaro: Gwamnati da hukumomin tsaro sun gaza, Gwamna Masari ya yi fallasa


Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce gwamnati da hukumomin tsaro sun gaza wajen tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya. Shafin isyaku.com ya samo.

Gwamna Masari ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa a kwanakin baya.

Yayin da yake amsa tambaya kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan, musamman yankin Arewa maso Yamma, Gwamnan ya ce

“Jami’an tsaro da mu gwamnati mutane ne suka dogara da su wajen kare su, kuma mun kasa yin hakan. Amma idan ka duba musabbabin gazawar an kashe jami’an tsaro da dama.

Har zuwa makonni biyu da suka gabata wani kwamishinan ‘yan sanda ya rasa ransa; wani sifeto ya rasa ransa; an kashe sojoji, jami’ai sun rasa rayukansu a kokarinsu na magance rashin tsaro.

Rashin tsaro bai shafi jihar Katsina kawai ba, ya shafi kusan kowace jiha a Najeriya, haka ma wasu makwabtan mu kamar Nijar da Mali su ma suna fama da wannan matsala.”

Ya kara da cewa an samu ci gaba a fannin gine-ginen tsaro a kasar

“An samu ci gaba ba kamar da ba, amma ba mu kai inda muke so ba kuma muna rokon Allah,” inji shi.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE