Type Here to Get Search Results !

Bayan Tinubu ya zabi Mataimakinsa, tsohon ɗan Majalisar tarayya da wani babban jigon APC sun yi murabus daga jam'iyyar


Wani babban jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon mamba a majalisar dokokin tarayya, Elder Chidi Wihioka, ya yi murabus daga jam'iyyar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne awanni 24 bayan wani tsohon muƙaddashin daraktan hukumar raya Neja Delta, Dame Ibim Semenitari, ya fice daga jam'iyyar APC.

Lokacin da ya rike kujarar ɗan majalisa, Wihioka, ya wakilci mazaɓar Ikwerre/Emuoha daga jihar Ribas majalisar dokoki ta tarayya.

Ya sanar da matakin murabus dinsa a wata wasika da ya aike wa shugaban APC na gundumar da ya fito Elele ta uku a jihar Ribas.

A wasiƙar, Honorabul Wihioka, ya bayyana cewa ya kai ga matakin ficewa daga jam'iyyar ne saboda yadda akalarta ta koma hannun mutum ɗaya, a cewarsa APC ta koma aljihunsa.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Ina son sanar da kai a hukumance cewa na yi murabus daga jam'iyyar All Progressive Congress, APC. Na ɗauki wannan matakin ne saboda yadda komai ya koma hannun mutum ɗaya kuma ina ganin shi ya mallaki APC a Ribas."

"Kuma mutumin ya hana zaman lafiya ya samu wurin zama a cikin jam'iyya ta hanyar ba kowane mamba damar taka rawar da ya dace. Zan sanar da jam'iyyar da na koma idan na gano wacce ta dace da ni."

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies