Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tabbatar da cewa ta sa ido a zaben fidda gwani da ya samar da Mohammad Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.
Kafin bayanin dai an yi ta cece-kuce kan wanda hukumar ta amince da shi a matsayin dan takarar gwamna tsakanin Abacha da Sadiq Wali
Kwamishinan Zabe (REC), Farfesa Riskuwa Shehu, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kano , a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, in ji jaridar The Guardian .
Kamar yadda a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani na PDP a Kano, Shehu Sagagi ne wanda doka ta amince da shi a matsayin shugaban jam'iyyar na jiha, wanda ya gudanar da zaben fidda gwanin da ya samar da Abacha."
Abacha ya kada Wali a zaben
Sai dai Abacha da Wali sun yi nasarar lashe zaben fidda gwani na PDP guda biyu a Kano, inda kowannen su ya yi ikirarin cewa shi ne sahihin dan takara.
Abacha ya samu kuri’u 736 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Jafar Sani-Bello, wanda ya samu kuri’u 710 a zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar Laraba 25 ga watan Mayu a jihar Kano.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI