Yanzu-yanzu: Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC, duba adadin kuri'u


Tsohon gwamna jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.

A zabensa na faako tun bayan barin muli a 2007, Tinubu yanzu shine zai wakilci jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

Tinubu ya lallasa yan takara 12 da suka fafata a zaben inda ya samu kuri'u sama da 1000

Wanda ya zo na biyu shine tsohon Gwamnan jihar Rivers, kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri'u 316.

Sannan Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya samu kuri'u 235.

Tinubu yanzu zai fafata da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP dss a ranar 25 ga Febrairu, 2023.

Ga jadawalin sakamakon:

S/N Sunayen yan takara Adadin Kuri'in da suka samu

1 Asiwaju Bola Tinubu 1213

2 Rotimi Amaechi 316

3 Farfesa Yemi Osinbajo 235

4 Ahmad Lawan 152

5 Yahaya Bello 47

6 Sani Ahmed Yarima 4

7 Ben Ayade 37

8 Rochas Okorocha 0

9 Tunde Bakare 0

10 Tein Jack Rich 0

11 Ogbonnaya Onu 1

12 Dave Umahi 38

13 Emeka Nwajuiba 1

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN