Yadda yar Najeriya ta aika kanta da kanta barzahu a kasar Gambia, duba dalili


Wata ‘yar Najeriya mai suna Sandra, ta kashe kanta a Gambia ta hanyar shan maganin kwari.

Kafar labarai na isyaku.com ya tattaro cewa lamarin ya faru ne a Bakoteh cikin karamar hukumar Kanifing da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Talata, 7 ga watan Yuni.

Har yanzu dai ba a iya tabbatar da lamarin da ya kai ta ga daukar matakin ba, amma a halin yanzu jami'an tsaro na gudanar da bincike kan lamarin. 

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ta kara da cewa matar ta rasu ne a wata cibiyar lafiya da ke kusa. 

"Na ji tana fama da tabin hankali, saurayin ya siya mata tikitin komawa Najeriya, lokacin da saurayin ya fita domin kammala shiriye shiruen tafiyarta zuwa Najeriya sai ta sha maganin kwari" Majiyar ta ce.

A halin da ake ciki kuma, mai shago, wanda ya sayar mata da maganin ga mamacin, ‘yan sanda sun kama shi.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE