Tsohon shugaban karamar hukumar Sokoto ya fice daga PDP ya koma APC


Shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, Alhaji Jelani Danbuga ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Sen. Aliyu Wamakko (APC- Sokoto) kan sabbin kafafen yada labarai, Malam Bashar Abubakar ya raba wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ranar Litinin a Abuja.

Abubakar ya ce, Wamakko wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar a jihar ya tarbi Danbuga cikin jam’iyyar APC ranar Asabar a Sakkwato.

Wamakko ya bayyana ficewa daga jam’iyyar “PDP a matsayin abin farin ciki kuma ya yi alkawarin za a dauke shi kamar kowane dan APC a koda yaushe.

Abubakar ya ce Danbuga ya samu rakiyar shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Sabon Birni, Alhaji Yawale Sarkin-Baki da wani tsohon kwamishina a jihar Alhaji Ahmad Barade da sauran sarakuna.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN