Da duminsa: Yadda saurayi ya yi wa budurwarsa zindir ya yi mata bulala tare da abokansa bisa zargin cin amana, duba abin da ya biyo baya (Bidiyo)


Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta fitar da hotunan Jimoh Abdulfatai, matashin da suka hada baki da abokansa suka ci zarafin budurwar sa, bisa zargin cewa ta yi masa magudi. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Fatai da abokansa sun daure wa budurwarsa hannu da kafafu suka dinga yi mata bulala akan zargin cewa tana kwanciya da wani. Ya ci gaba da cire wandonta ya yi mata bulala a duwawunta ba wando sannan ya saka bidiyon a yanar gizo. 

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Okasanmi Ajayi ya fitar a yau 23 ga watan Yuni, ya ce an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Sanarwar ta ce;

‘’Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara na son sanar da jama’a matakin da ta dauka cikin gaggawa domin mayar da martani ga wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta da na yanar gizo da kusan kowane lebe jiya, inda ya nuna wata budurwa mai suna Ayomide Afolayan, da sauran bayanai. An tsare ta, an ga yadda ake aiwatar mata da mugun nufi, rashin zuciya da rashin mutunci da ake zargin saurayinta mai suna Jimoh Abdulfatai da ke garin Shao a karamar hukumar Moro a jihar Kwara ya yi mata.

Tare da taimakon abokansa sun damke hannayenta suka aiwatar mata da cin mutunci. Wadanda aka kama sun hada da wasu abokanan wanda ake zargi na farko mai suna, Olamide Babatunde, Afeez Ayomide, Agboola Abdulsamad da Yakubu Mustapha, inda suka yi mata mummunar illa.

Yansanda sun dira wajen da abin yake faruwa suka yantar da yarinyar kuma suka kai ta asibiti aka yi mata magani.

Kwamishinan ‘yan sanda, Cp Tuesday Assayomo psc (+), ya ba da umarnin mika lamarin ga CID na rundunar domin yin bincike mai zurfi da kuma kan lokaci. 


Wadanda ake zargin dai sun amince da aikata laifin, kuma dalilin da ya sa suka aikata wannan aika-aika, wani zargi ne kawai na rashin imani daga bangaren yarinyar wanda ta musanta. Duk da musanta zargin, saurayin ya karbo wayar matar da karfi sannan ya mika wayar ga daya daga cikin abokansa don ya fara daukar hoton bidiyon da kuma yadawa a shafukan sada zumunta.

Binciken da aka yi, an gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu kuma an tsare su a gidan yari har zuwa lokacin da za a saurari shari’ar da ta dace.

Wannan zai kawo cikas ga wasu mutane masu irin wannan mugun hali a zukatansu.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kwara, yana so ya yi amfani da wannan damar wajen nasiha ga iyaye kan bukatar zama iyaye a zahiri; ya kamata iyaye su sanya ido a kan ‘ya’yansu, su san irin abokan da suke hulda da su domin gujewa irin wannan mugunyar al’amari.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN