Gwamnan Imo ya ba yan bindiga kwanaki 10 su miƙa wuya ko su sha ruwan bama-bamai


Gabanin ziyarar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zuwa Imo ranar 12 ga watan Yuli, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, ya ba 'yan bindiga da suka hana zaman lafiya wa'adin kwanaki 10 su miƙa wuya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Uzodinma ya shawarci 'yan bindigan su bar dazukan jihar kuma su miƙa wuya tare da damƙa makamansu ga Sarakunan gargajiya don a yafe musu.

Da yake jawabi ga manema labarai a Owerri, Gwamnan ya ce jihar Imo zata karɓi bakuncin bikin shekara-shekara na sojojin Najeriya daga 30 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli.

A cewarsa, akalla dakarun tsaro 10,000 daga hukumar sojojin ƙasa, na sama da na ruwa da kuma yan sanda, zasu halarci bikin.

Gwamnan ya ƙara da cewa jihar Imo zata karɓi sabbin kayan aikin jami'an tsaro, waɗan da za'ai amfani da su wajen share ƴan bindiga a wuraren da suke ɓuya cikin dazuka daban-daban a faɗin jihar.

Vanguard ta rahoto Uzodinma ya ce:

"Jihar mu ta shirya fiye da baya domin kakkaɓe baki ɗaya 'yan bindiga, don cimma haka zamu tanadi sabbin kayan aiki kuma zamu ɗauki ƙarin dakarun Ebube-Agu da zasu yi aiki tare da hukumomin tsaro."

"Zasu tsaftace dukkan hanyoyin ruwa da kuma yan bindiga haɗi da ɓarayin mai. Duk hanyoyin ruwan mu zasu kasance cikin kula da zaran kayan aiki sun isa ga sojojin ruwa a sansanin su na Oguta."

Ayyukan da Buhari zai yi yayin ziyara a Imo

Uzodinma ya ce shugaban kasa, wanda ake tsammanin zai buɗe bikin ranar ta Sojoji, ya zaɓi ranakun 12 da 13 ga watan Yulin domin buɗe da wasu ayyuka.

A cewar gwamnan Buhari zai buɗe hanyoyin Owerri-Orlu da Owerri-Okigwe, kana ya kaddamar da fara aikin hanyar Owerri-Mbaise-Umuahia (daga hukumar kashe gobara) da hanyar Orlu-Akokwa.

Wannan na zuwa ne a karshen makon nan yayin da jama'ar yankin ke kokarin fara ayyukansu na gona.

Wani mazaunin yankin ya bayyana dalla-dalla yadda lamarin ya faru da kuma irin cin amanan da suka fuskanta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN