Biodun Oyebanji, tsohon sakataren gwamnatin jihar Ekiti, ya tabbata wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti.
Kayode Oyebode, baturen zaben da aka yi a ranar Asabar, ya sanar da sakamakon zaben a sa'o'in farko na ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.
Oyebanji ya samu kuri'u 187,057 inda ya lallasa manyan masu kalubalantarsa, Segun Oni na jam'iyyar SDP wanda ya samu kuri'u 82,211 da Bisi Kolawole na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 67,457.
Fafesa Kayode Oyebode, baturen zaben, ya bayyana Oyebanji a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben a wurin karfe 3:04 na safiyar Lahadi.
Jimillar 'yan takara 16 ne aka samu suka yi takarar kujerar gwamnan. An samu kuri'u masu amfani 351,865, kuri'u da suka lalace 8,888 sai jimillar kuri'un da aka kada sun kai 360,753.
Ga sakamakon karashe na zaben:
A: 166
AAC: 409
ADC: 5,597
ADP: 3,495
APC: 187,057
APGA: 376
APM: 290
APP: 1,980
LP: 195
NNPP: 529
NRM:347
PDP: 67,457
PRP: 856
SDP: 82,211
YPP: 618
ZLP: 282