Da dumi--dumi: 'Yan sandan jihar Kebbi sun kama wanda ya kashe wata mata a dakin Otal a garin Zuru


Rundunar Yan sandan jihar Kebbi ta kama Bashir Mohammed dan shekara 22 wanda ake zargin ya kashe Jennifer Goje a garin Zuru
. Kafar labarai na intanet isyaku.com ya samo.

Jennifer ta rasa ranta ne a dakinta da ke River Side Hotel a Unguwar Zuru ranar Juma'a 3 ga watan Yuni 2022. An sami gawarta kwance cikin jini tare da raunukan sukan wuka a wasu sassa a jikinta cewar wata majiya.

Kakakin rundunar yansandan jihar Kebbi SP Nafi'u Abubakar ya ce

 "Tabbas mun kama wanda ake zargi ya kashe matar. Jami'an mu sun bi shi har Kano aka kamo shi, aka dawo da shi Zuru, daga bisani aka kawo shi Shelkwatar yansandan jihar Kebbi   varin Birnin kebbi, kuma ana gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka SCID".

Yanzu dai binciken yansanda ne kadai zai tabbatar da hakikanin abin da ya faru har Wanda ake zargi ya kashe Jennifer. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN