Da dumi-dumi: An kama magidanci da sassan jikin mutum a Zamfara


 Yan sandan jihar Zamfara sun yi ram da wani da ake zargin 'dan sa kai ne bayan an kama shi da sassan jikin mutum, Channels TV ta ruwaito.

A wata takarda da rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta fitar a ranar Litinin ta bayyana yadda ake zargin Jabiru Ibrahim daga gundumar Dauran a cikin karamar hukumar Zurmi ta jihar.

"Hadin guiwar 'yan sanda da jami'an tsaron da ke yaki da ta'addanci tsakanin Dauran zuwa Zurmi sun yi ram da wanda ake zargin gami da mika shi hedkwatar rundunar 'yan sandan da ke Gusau don cigaba da bincikarsa,"

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan, Muhammad Shehu ya bayyana a takardar.

A iya binciken da aka gabatar, ya bayyana yadda wanda ake zargin yake cikin kungiyar 'yan sa kai wadanda suka dauki tsawon lokaci suna cin karensu ba babbaka a yankin Dauran tare da daukar doka a hannunsu, wanda ke janyo 'yan bindiga yawan kai hare-haren daukar fansa ga mutanen yankin ba su ji ba ba su gani ba.

"Yayin da aka kama wanda ake zargin, ya bayyana yadda shi da wasu uku daga cikin 'yan kungiyarsu suka yi wa wani Abdullah, bafulatani kisan gilla, daga bisani wanda ake zargin ya yanke hannun daman mamacin."

Har ila yau, ana cigaba da bincike don cafko sauran abokan harkallarsa tare yi wa lamarin garanbawul kafin a gurfanar da su gaban kotu, a cewarsa.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE