Wasu jami'an tsaro mata daga hukumar yan sanda da kuma hukumar Cibil Defence NSCDC sun bai wa hammata iska a wurin taron APC da ke gudana a Abuja.
A wani Bidiyo da ya watsu a kafar sada zumunta ya nuna yadda jami'an mata suka dambaci bayan wani ɗan saɓani a shiga tsakanin su yayin da suke aiki a Eagle Square.
Sauran jami'an tsaro da ke kusa da wurin sun yi gaggawar shiga tsakani domin raba su amma jami'ar NSCDC ɗin na ƙara shigewa
Kalli Bidiyon anan:
https://mobile.facebook.com/watch/?v=1396286404171421&_rdr
A yau Laraba, rana ta uku tun bayan fara harkokin zaɓen fidda gwanin APC, bayanai sun tabbatar da cewa an kammala zaɓe kuma yanzu haka ana aikin ƙidaya kuri'u.
Rubuta ra ayin ka