Bam ya tarwatse da yan IPOB guda biyu da suka binne domin cutar da sojin Najeriya


Rundunar sojin Najeriya ta ce wani bam da aka dasa da ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da reshenta masu dauke da makamai, wato Eastern Security Network (ESN) suka binne ta tarwatse, wanda ya yi sanadin jikkatar mambobinta
.

Fashewar ta yi sanadin jikkata wasu ‘yan kungiyar guda biyu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu, ranar Alhamis a Enugu.

Nwachukwu ya ce lamarin ya faru ne a hanyar Eke Ututu zuwa Orsu a karamar hukumar Orsu ta Imo a ranar 1 ga watan Yuni.

“Ba da gangan ba ‘yan kungiyar sun taka bam din da suka dasa a kan wasu hanyoyi a Orlu da ke karamar hukumar Orsu, a lokacin da suke kokarin gujewa farmakin da sojoji ke kaiwa ‘yan ta’adda a yankin.

“Haramtacciyar kungiyar ta dasa bama-bamai a kan hanyoyin da sojoji ke sintiri a kokarin da suka yi na kawo illa ga sojojin.

"Muna kira ga duk masu son zaman lafiya na Kudu-maso-Gabas da su sanar da sojoji wuraren da za a iya binne wadannan bama-baman don fitar da su da kuma kawar da su," in ji shi. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN