Yanzu: Kotu ta ba da belin Okorocha a zargin almundahanar N2.9bn da ke kansa


 Yanzun nan muke samun labari da duminsa daga kafar labarai ta Channels Tv cewa, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha da ke fuskantar shari'a da hukumar EFCC.

Idan baku manta ba, mun kawo rahotanni a baya da ke bayyana yadda jami'an hukumar yaki da yiw atattalin arzikin kasa ta'annuti (EFCC) suka dura gidan Okorocha kana suka tafi dashi.

Bayan haka, aka ce an gurfanar dashi a gaban kotu, amma batun belinsa ya ci tura saboda wasu dalilai.

A rahoton baya-bayan nan, an ce daga karshe an ba da belinsa.

Belin nasa na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar APC ke ci gaba da tantance 'yan takarar shugaban kasa da suka sayi fom kwanan nan.

Okorocha na daga cikin wadanda za a tantance a yau Talata, kamar yadda wani jerin sunayen wadanda za a tantance a ranar ya nuna.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN