Wasu limaman cocin Katolika guda biyu da direbansu da kuma mata da miji sun kone kurmus a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a jihar Anambra.
Hadarin da ya hada da wata motar bas Toyota Hiace da Toyota Highlander ya afku ne a kan titin Nawfia na babban titin Enugu zuwa Onitsha a daren ranar Talata, 12 ga watan Afrilu.
Bincike ya nuna cewa Limamai Mata da lamarin ya rutsa da su da aka bayyana sunayensu sun hada da Rabaran Sr. Virginia Obike da Sr. Monica Ilem, dukkansu shugaba ne da Bursar na makarantar Handmaid, Amansea, da ke karamar hukumar Awka ta Arewa, da direban su Mista Chamberlain Umunakwe, suna tafiya Kan hanyarsu ta zuwa garin Amansea ne daga garin Ifite-Ogwari.a karamar hukumar Ayamelum, inda suka je siyan buhunan shinkafa don amfanin makarantar.
Sauran wadanda abin ya rutsa da su a daya mota kirar Toyota Highlander sun hada da Mista Emmanuel Okeke, tsohon ma’aikacin gwamnatin jihar Anambra, da matarsa.
Mista Ifeanacho Okeke, wanda ya yi magana a wurin da hatsarin ya faru, ya ce ya tattauna da dan uwansa Emmanuel da misalin karfe 5 na yammacin jiya, kuma da misalin karfe 9 na dare aka kashe layinsa da na matarsa, lamarin da ya sa aka gudanar da bincike tare da gano abin bakin ciki da ya auku da sanyin safiyar yau.
Wani ganau mai suna Mista Chinecherem Okonkwo daga Nawfia, ya ce ya isa wurin da hatsarin ya afku ne a jiya da daddare a lokacin da ake ruwan sama a lokacin da motocin ke ci gaba da ci da wuta, amma an makara domin samun taimako mai ma’ana.
An ga ‘yan uwa maza da mata tare da wasu jama'a a wurin da hatsarin ya afku, yayin da wasu kuma suka taimaka wajen dauke motocin daga titin.