Uba da dansa sun mutu a hatsarin mota a Nasarawa, duba yadda ta faru


Wani dattijo mai shekaru 63, Cif Likita Gyado da dansa, Joe Gyado sun mutu a wani hadarin mota da ya rutsa da su a jihar Nasarawa.

An tattaro cewa hatsarin ya afku ne a Gwanje da ke karamar hukumar Akwanga ta jihar a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilu. 

Marigayi Gyado shi ne tsohon ma'ajin fadar Chun Mada. 

Mai amfani da Facebook, Barr. Wanche Christian Magani, ya tabbatar da wannan labari mai ban tausayi a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 5 ga Afrilu. 

Ya ruwaito cewa:

"A Madadin Kaina (Barr.Wanche Christian Magani) da Tawagar Kamfen na, Muna Jajantawa Iyalin Marigayi. Mr Likita Gyado Meshiru, da Al'ummar Rija, Anchor Ward na karamar hukumar Akwanga, ya ce ba a shirya mutuwa ba! yace.

“Marigayi Likita Gyado Meshiru ya rasu ne tare da dansa, a unguwar Gwanje da ke hanyar Jos.

"Barr. Wanche Christian Magani yayi addu'ar Allah madaukakin sarki ya gafartawa dukkan kurakuran su da aka sani da wanda ba a san su ba, ya kuma saka masa da rahamar sa marar iyaka ya kuma ba shi huta ta har abada.

"Barr.Wanche Christian ya kara da cewa mutuwa ba makawa ce kuma ga kowa da kowa ya fi dandana mutuwa, yana addu'ar Allah ya baiwa iyalai gaba daya karfin jure wannan rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba a matsayin kaddara daga Ubangiji kuma ya sa namu sauki idan ta zo." 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN