An kama wanda ya kashe babban abokinsa ya gudu da motarsa da kudinsa N2m a jihar Neja


Rundunar yansandan jihar Niger ta sanar da samun nassarar cafke wani mutum da take nema ruwa jallo bayan ya kashe abokinsa ya gudu da kudinsa N2m da motarsa Peugeot 206.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu, ya ce an kama Bashir ne tare da dan uwansa Aliyu Ibrahim, a wani otal da ke Minna yayin da aka kama wani Abdullahi Garba da laifin siyan wayar mamacin. .  

Bashir ya amince da aikata laifin, inda ya kara da cewa shi da dan uwansa sun hada baki da wani mai suna Suleiman Mahmud domin su kai wanda aka kashen zuwa gidansa don yin wata sana’ar kasuwanci

A lokacin da marigayi dan kasuwar ya isa gidan, wadanda ake zargin sun daba masa wuka har lahira sannan suka gudu da motarsa ​​dauke da kudi N2m. 

Yanzu haka yansanda na gudanar da bincike da niyyar gurfanar da su a gaban Kotu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN