Kebbi: Dan NYSC ya yanke jiki ya fadi ya mutu a garin Dakin Gari yayin da yake kallon gasar kwallon kafa, duba yadda ta faru (Hotuna)


Wani dan yi wa kasa hidima NUSC mai suna Musa Momoh Tunde mai lambar aikin yi wa kasa hidima (KB/22A /2278 ya rasu yayin da yake kallon kwallon kafa a sansanin masu yi wa kasa hidima a garin Dakin Gari a jihar Kebbi.

Tunde ya karanci Public Administration a Federal polytechnic Bida, ya yanke jiki ya fadi ya mutu ranar Juma'a 26 ga watan Maris 2022 yayin da yake kallon gasar kwallon kafa da ake bugawa a cikin sansanin.

Darakta janar na NYSC na kasa Major-General Shuaibu Ibrahim ya aike sakon ta'aziyya ga iyalin Tunde.

An bizine Tunde a babbar Makabartar jihar Kebbi da ke garin Birnin kebbi.Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN