Yan Majalisa Suna Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara


Yan Majalisar Jihar Zamfara sun fara shirye-shiryen tumbuke mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Gusai, daga mukamin shi, Channels TV ta ruwaito.

Hakan ya biyo bayan wata takarda ta kora ga mataimakin gwamnan wanda aka gabatar ga kakakin majalisar.

Mahdi Gusau: 'Yan majalisa sun shirin tsige mataimakin gwamnan Zamfara kan zargin rashawa

Mahdi Gusau: 'Yan majalisa sun shirin tsige mataimakin gwamnan Zamfara. Hoto: Channels Television Source: Twitter

Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar, Musa Bawa, ya gabatar da takardu ga kakakin majalisar, Nasiru Mu’azu a ranar Juma’a a farfajiyar majalisar da ke Gusau, babban birnin jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai ba a san dalilin mataimakin kakakin majalisar ba wanda ya maimaita shugabancin kwamitin asusun gwamnati ba na daukar wannan matakin.

Ana zargin Mahdi da handamar dukiyar al’umma

Channels TV ta tattaro bayanai akan yadda majalisar ta zargi mataimakin gwamnan da yin karantsaye ga kundin tsarin mulki, tozarta mukaminsa da kuma satar kudade.

A cewar Bawa yayin gabatar da takardun a wani kwarya-kwaryan taro da suka yi a ofishin kakakin:

“Ina gabatar da wannan takardar ga kakakin majalisa, Nasiru Mua’zu Magarya akan tumbuke mataimakin gwamnan Jihar Zamfara.”

Lokacin da Mu’azu ya amshi takardun ya yi alkawarin duba takardun inda yace zai dauki mataki daidai da abinda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Sun fara samun matsaloli ne tun bayan gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya koma APC

A cewarsa:

“Ka zo nan ofishi na, mataimakin kakakin majalisa kuma shugaban kwamitin asusun gwamnati, kuma ka gabatar min da takardun cire mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Gusau.

“Na amsa kuma ina mai tabbatar muku da cewa zan yi aiki bisa yadda kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka gyara a 1999 ya tanadar.”

Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ci gaba da nuna rashin yardarsa akan abubuwa da dama tun bayan gwamnan ya sauya jam’iyya.

Matawalle ya zama gwamna a karkashin jam’iyyar PDP kuma tun watan Yunin shekarar da ta gabata ya sanar da komawarsa APC.

Yayin da kowa ya yi tunanin mataimakinsa zai bi sahun sa, Gusau ya bayyana a taron PDP inda ya ce yana nan a jam’iyyar babu gudu babu ja da baya.

================

Daga Jaridar iyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook fFacebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN