Tap di: Saurayi ya aika wa mijin budurwarsa hoton tsiraicinta, duba abin da ya faru


Ana tuhumar wani dalibi dan kasar Kenya mai shekaru 21 da zargin kan cin zarafin mijin wata wacce ake zargi da zama masoyiyar sa, bayan ya tura mishi hoton tsiraici na sirrin matar sa.

Wanda ake zargin, Steven Wanjohi Kamande, ya bayyana gaban babban alkalin majistare Wendy Kagendo na kotun shari'a ta Milimani a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Ya musanta laifuka ukun da ake zargin sa da su, na tura mishi bayanin kanzon kurege, barazana ga rayuwar shi da gangancin yada ababen da basu dace ba.

Kotun ta ji yadda Wanjohi, wanda dalibi ne a wata jami'a a cikin birnin, ya karya doka ta hanyar yada hotunan sirrin, wanda ke nuna Esther Nduta Githinji da niyyar firgita ta da mijin ta Joel Thuo.

An zargi wanda ake tuhumar da tura hotunan sirrin matar ga mijinta, a matsayin shaidar yana lalata da ita.

Haka zalika, an tuhume shi da gangancin yada hotunan tsiraici da na sirrin Nduta, matar mutumin da yake korafin wanda ya san ba gaskiya bane, inda ya yada don firgitar wa ga Thuo da iyalin shi.

An zargi wanda ake tuhumar da tura hotunan ta shafin sa na Facebook a kwanaki daban-daban tsakanin 1 ga watan Mayun 2021 da 14 ga watan Janairun 2022, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Takardar dake dauke da karar Wanjohi ta bayyana kalamai kamar haka:

"A kwanaki daban-daban a wurin da ba a ambata ba ta hanyar ganganci an wallafa labarin kanzon kurege, inda aka ce 'unasemanga uki na bibi' ta hanyar amfani da shafin ka na Facebook, Steven Kamande zuwa ga Joel Thuo Mwangi duk da an san ba gaskiya bane, an yada don firgitar wa gami da razanar wa ga Joel da iyalin shi."

An cigaba da tuhumar wanda ake zargin da laifi na uku, na barazanar yi wa Nduta kisan kare dangi, tsakanin lokuta irin wannan a wani wuri da ba a sani ba, cikin Jamhuriyar Kenya bayan bayyanar labarin.

Bayan musanta laifukan da ake tuhumar shi da su, an bayar da belin wanda ake zargin da sharuddan zai cike duk ka'idojin da kotun ta gindaya mishi.

An kuma bukaci ya gabatar da shaidu a za a iya bukata yayin cigaba da sauraron karar shi.

Shari'a ba ta haramta sakin shi ba, yayin da kotun Majistaren ta yi umarni da sakin shi tare da biyan Ksh100,000 ko kudin beli kwatankwacin haka da gabatar da mutum daya tabbatacce.

Matashi mai shekaru 19 ya dirka wa malamar shi mai shekaru 28 ciki, za ta haife shi

A wani labari na daban, Richard Nana Sam, dan kasar Ghana ne wanda ransa yayi matukar baci, sanadiyyar wani lamari dake wakana a gidan shi, wanda ya yanke shawarar fallasa wa a kafafan sada zumuntar zamani, da sa ran samun mafita.

Yayin bada labarin kalubalen da yake fuskanta a wata sananniyar kungiyar 'yan Ghana dake da shafi a Facebook, ya kwashe labarin tun daga farko har karshe.

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN