Da Duminsa: Wata dalibar Jami'a a ta faɗa shadda a dakin kwana na dalibai mata, ta rasu, duba yadda ta faru


Ɗalibar 200-Level a sashin koyon harsunan Afirka na jami'ar Obafemi Awolowo University, dake Ile Ife, Ajibola Ayomikun, ta rigamu gidan gaskiya bayan ta faɗa Shadda.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Ayomikun ta faɗa Shadda ne a ɗaya daga cikin gidan kwanan ɗalibai na wajen makaranta mai suna BVER, dake Student's Village.

Kakakin jami'ar Obafemi Awolowo, Abiodun Olarewaju, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya bayyana cewa jami'a baki ɗaya ta shiga jimami da takaici kan abin da ya faru da ɗalibarta mara daɗin ji.

The Cable ta rahoto ya ce:

"Lokacin da muka samu labari, nan take muka haɗa tawagar taimakon gaggawa a jami'a, jihar Osun da kuma Asibitin koyarwa, wanda suka yi namijin kokari har suna fito da ita."

"Ba tare da ɓata lokaci ba aka tafi da ita Asibitin koyarwa na jami'ar OAU, iɓda aka tabbatar da rai ya yi halinsa."

Wane mataki jami'a ta ɗauka?

Mataimakin shugaban jami'ar (VC), Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya jajantawa sauran ɗalibai yayin da ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamaciyar.

VC, wanda ya bayyana lamarin da ba za'a amince ba, ya sha alwashin gudanar da bincike kan musabbabin da ya jawo mutuwar ɗalibar kuma a ɗauki mataki kan duk wanda aka gano yana da hannu.

Ogunbodede ya bukaci ɗalibai su kwantar da hankulan su kuma su bi doka sau da kafa yayin da jami'an yan sanda suka shiga lamarin domin gudanar da bincike.

Source: Legit.ng

================

Daga Jaridar isyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook Facebook.com/isyakulabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN