Hukumar yan sanda reshen jihar Rivers ta kama wani matashi, Kelechi, wanda aka gano gawar masoyiyarsa a gidan da suke zaune.
Jaridar Punch ta rahoto cewa an tsinci gawar budurwan ne a gidansu dake layin Woke a kan hanyar Chirubim, Diobu, a Patakwal.
Kakakin hukumar yan sandan, SP Grace Iringe-Koko, ranar Litinin, tace yanzun haka ana tsare da mutumin a sashin binciken manyan ƙaifuka (SCID).
Iringe-Koko ta bayyana cewa kwamishinan yan sanda na jihar Ribas, Friday Eboka, ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike kan wanda ake zargin.
A cewar kwamishinan mutumin ya san yadda aka yi budurwarsa, Ifeoma Uzoigwe, ta rasa rayuwarta da kuma abin da ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Meya faru budurwar ta mutu?
Tun a watan Disamba, 2021, aka gano gawar matar yayin da ta fara ruɓewa kuma warin ta ya mamaye makotan gidajen dake layin.
Wata majya daga hukumar yan sanda ta shaida wa manema labarai cewa Kelechi, ya gudu daga Anguwar baki É—aya tun kafin mutane su gano gawar matar.
Mai kula da yankin, Chinonye Anurum, ya ce yan sandan ofishin Nkpolu sun kama wanda ake zargin ne bisa taimakon iyalansa, waɗan da suka gano inda ya ɓoye bayan wata ɗaya da faruwar lamarin.
Ya ce:
"Yan sanda sun miƙa Kelechi ga sashin SCIID, kuma an sake kira na domin ba da rahoto kan lamarin bayan na farko da na rubuta a watan Disamba."
Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari , ta shiga jerin yan Najeriya dake kiran a ɗauki tsattsauran mataki kan makasan Hanifa Abubakar.
Aisha Buhari ta bayyana goyon bayanta kan hukuncin kashe mutumin da ya kashe Hanifa a bainar jama'a domin hakan ya zama darasi ga yan baya.
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook facebook.com/isyakalabari