Labarin yadda ya'yan tsohon hafsan sojin Najeriya suka maka kawun su a gaban kotu kan Gado


Ya'yan marigayi hafsan sojojin ƙasa a Najeriya, Janar Luka. N Yusuf, sun gurfanar da kawunsu, Emmanuel Yusuf, a gaban kotun majistire dake zamanta a Kaduna.

Leadership ta rahoto cewa ƴaƴan marigayin sun bukaci kotu ta kwato musu hakkin su na wata kadara da kawun su ke neman kwace wa.

A karar mai lamba KDC/734cc/21 da Bilhatu Beauty Yusuf, ya shigar a madadin yan uwansa, ya roki kotu ta taimaka musu wajen dawo musu da hakkin su.

A cewarsa, kadarar na nan a No. 15, kan hanyar Bourmediene, Anguwar Narayi High Cost, cikin garin Kaduna, kuma a halin yanzun kawun su ke amfani da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lauyan masu shigar da ƙarar, Barista D.B. Kwajaffa, ya bayyana cewa waɗan da yake kare wa suke da haƙƙin mallakar kadarar gidan mahaifinsu dake Narayi a Kaduna.

Amma wanda ake ƙara ya mallake gidan da sunan yana da lasisin mallaka, wanda tuni aka soke lasisin tun a ranar 25 ga watan Oktoba. 2021, inji Lauyan.

Ta ya dukiyar taje hannun kawunsu?

Karar mai ɗauke da sakin layi 15, ta yi bayani dalla-dalla a sakin layi na 9 cewa, wanda ake ƙara ya samu izinin zama a wannan wuri da ake cece kuce daga marigayya mahaifiyar masu ƙara, Bilki Mary Yusuf.

Wani sashin takardan karar yace:

"Ƴaƴan marigayi COAS sun baiwa kawun nasu wa'adi ya tashi daga wurin a rubuce, domin dawo da dukiyar su, amma ya ƙi, ya yi watsi da lamarin."

Emmanuel Leweh, ciyaman na ƙaramar hukumar Akwanga, dake jihar Nasarawa, ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi jim kaɗan bayan fitowa daga taro.

Mista Leweh, wanda ya kwashe watanni uku kacal a ofishin ciyaman na Akwanga, ya mutu ne a wani Asibitin kuɗi dake babban birnin tarayya Abuja , ranar Alhamis.

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN