Gwamna ya tona asiri: Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle


Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce daga cikin dalilan da suke assasa wutar ta'addanci akwai kyale 'yan bindigar da 'yan ta'adda da ake yi babu wani hukunci. 

A cewar gwamnan, sau da yawa ana sakin 'yan bindigan daji ba tare da an yi musu wani hukunci ba, Daily Trust ta ruwaito. 

Matawalle ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin da ya karba wakilan gwamnatin tarayya yayin da suka je masa ziyarar jaje kan hare-haren da aka kai wa wasu yankunan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar. 

Wakilan gwamnatin tarayyan sun samu shugabancin ministan tsaro, Manjo janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, mai bada shawara kan tsaron shawara, Manj Janar Babagana Munguno, Sifeta Janar na 'yan sanda, Usman Baba Alkali. 

Sauran sun hada da ministan lamurran 'yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, ministan walwala da jin kan 'yan kasa, Sadiya Umar Farouk da mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa, Malam Garba Shehu. 

Kamar yadda yace: "Wata matsala da muka gano duk da kokarin dakarun sojin shi ne, basu da makaman zamani wadanda za su dinga yakin da su. Tabbatar da yakin zamani kuwa ya dogara da kayan aiki na zamani. 

Akwai matukar amfani idan aka samar wa dakarun nan kayan yaki na zamani domin su samu nasara kan 'yan bindigan Zamfara da arewa maso yammaci." 

"Alamu sun suna cewa, har sai an samar da isassun kayan aikin zamani sannan hukumomin tsaro zasu iya yakar ta'addanci yadda ya dace. 

Ana iya ganin wannan daga kiraye-kirayen da wasu shugabanni suke wa jama'arsu kan su nemi makamai domin bai wa kansu kariya. 

"Al'amarin gaggawa, gwamnatin tarayya ta samar da makamai kuma ta tura su dukkan sassan kasar nan. Idan har makamai dubu za a iya samarwa, za su yi matukar amfani wurin sauya akalar yaki da 'yan bindiga a cikin kankanin lokaci da izinin Allah. 

Ina son janyo hankalin gwamnatin tarayya kan cewa, asusan da ke daukar nauyin ta'addanci a sassan arewa suna da alaka. A wasu misali, akwai shaidar cewa akwai alaka tsakanin Boko Haram da wasu kungiyoyin ta'addanci na arewa maso yamma. 

Ina son karawa da cewa, duk wani tsari da za a fitar na yaki da 'yan bindiga da duk wasu nauyin ta'addanci, ya mayar da hankali a jihar Zamfara. Dajikanmu sun zama madaddalar 'yan bindiga wanda daga nan suke shiryawa tare da kaddamar da farmaki a sauran sassan arewa maso yammaci," ya kara da cewa 

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN