Da duminsa: An sako daliban Birnin Yauri da aka sace a Kebbi bayan watanni 6, duba yadda ta faru


Rahoton Daily Trust ya ce, dalibai 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi da kuma malami daya na makarantar, sun samu ‘yanci bayan watanni shida da aka yi garkuwa da su. 

A ranar 17 ga watan Yuni, 2021, wasu ‘yan bindiga daga dajin Rijau da ke makwabtaka da jihar Neja, sun kutsa cikin makarantar tare da yin garkuwa da dalibai da ma’aikata. 

Yan bindigar wadanda rahotanni suka ce sun mamaye makarantar ne a kan babura, sun yi fatattaki jami’an tsaron da ke wurin, inda suka kashe dan sanda nan take.

 Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi ya yi watsi da tattaunawa da ta'addan da ke neman kudin fansa. 

Watanni hudu bayan sace su, an sako malamai uku da dalibai 30 amma babu tabbas ko an biya kudin fansa. 

A ranar Asabar din da ta gabata ne mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya tabbatar da sakin wasu dalibai 30 da malaminsu. 

"A yau Asabar 8 ga watan Janairu, 2022 dalibai 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri da malami daya sun isa Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi bayan an sako su. Za a duba lafiyarsu tare da tallafa musu kafin daga bisani a sake hada su da iyalansu".

 “Za a iya tunawa a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba, 2022, an sako daliban makarantar guda 30, aka kawo su Birnin Kebbi domin a sada su da iyalansu. 

"Muna godiya ga dukkan hukumomin tsaro da wadanda suka taimaka wajen ganin an sako su, yayin da muke taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar nasarar da aka samu." 

Ya zuwa yanzu, an sako dalibai 57 da malaman kwalejin 4, inda aka tara da wadanda aka sako a watan Oktoba, kamar yadda The Guardian ta rahoto. 

Yawan hare-haren da ake kaiwa ya zama abin damuwa ga 'yan Najeriya ganin yadda kungiyoyin 'yan ta'adda ke kai hare-hare a fadin kasar duk kuwa da kokarin da da gwamnati da jami'an tsaro suka ce suna yi. 

A daya daga cikin irin wadannan hare-hare, 'yan bindiga masu gudun hijita sun kashe mutane sama da 143 a jihar Zamfara. 

Tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, inda ya sha alwashin cewa za a zakulo wadanda suka yi barnar. 

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN