Da duminsa: Ganduje ya mayar wa Kwankwaso kakkausar martani kan wani zance na 2019, duba ka gani



Gwamnatin jihar Kano ta yi kaca-kaca da maganar murdiya da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai ci zaben gwamna a 2019 ba, Daily Nigerian ta rahoto kawai ya yi makudi ne. 

Cece-kucen da aka samu na zuwa ne kwana guda bayan da Ganduje ya yi tsokaci, a cikin sakonsa na sabuwar shekara, kan sasantawa da ubangidan nasa Kwankwaso. 

Martanin Ganduje ya zo ne cikin wata sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na jihar Muhammad Garba, ya fitar. 

Sanarwar ta ce sabanin ikirarin Kwankwaso, tsohon gwamnan ya jagoranci wani shiri na magudin zabe, musamman a kananan hukumomi, inda matasa, galibi da ba su da ko katin zabe suka shiga layin kada kuri'a. 

Ya ce a fili yake cewa, sa’o’i kadan da fara kada kuri’a aka ce akasarin akwatunan zabe an cika su, daga baya INEC ta gano cewa ba a yi amfani da na’urar tantance masu zabe ba. 

Hakazalika, ya zargi cewa, ba tantance masu zabe ba don haka dole ne ma hukumar ta INEC ta soke sakamakon zabe daga cibiyoyi da yawa tare da ayyana zaben a matsayin wanda ba a kammala ba 

Garba ya yi nuni da cewa, abin takaici ne yadda Kwankwaso a matsayinsa na jagoran da ke da hannu a cikin zaben, har yanzu yake magana kan batun sakamakon zaben da hukumomi suka gudanar kuma kotu ta amince da shi. 

Kwamishinan ya ce kwanaki kadan da suka gabata Kwankwaso ya bayyana a kafafen yada labarai yana gargadin mabiyansa kan kalaman da basu dace ba amma sai ya gashi da kansa fadin irinsu 

Ya ce bisa ga dukkan alamu, a hirar Kwankwaso ya yi yunkurin bata gwamnatin Ganduje da cewa ta yi masa illa fiye da alheri, wanda kwata-kwata ya saba da'awar hakikanin zaman lafiya da sulhu da ya fada wa mabiyansa a ‘yan kwanakin nan. 

Malam Garba ya bayyana cewa, kamata ya yi Kwankwaso ya gode wa Ganduje bisa kammala ayyukan da ya yi watsi da su. 

Ya kuma kara da cewa al’ummar Kano sun ci gajiyar tsarin Ganduje na ci gaba da da ayyukan da aka bari tare da kammala su cikin shekaru shida a jihar 

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN