Cin amana: Yadda mai tsaron shago ya yi ɓadda-kama, ya yi barazanar sace mai gidansa, ya nemi a bashi N1.5m


Jami’an hukumar NSCDC na jihar sun samu nasarar kama wani mai tsaron shago, Tobiloba Olayinka, bisa zarginsa da shirya kulle-kullen garkuwa da mai shagon da yake tsaro duk don tatsar N1.5m daga wurinsa, The Punch ta ruwaito. 

Kwamandan NSCDC na jihar, Mr John Fayemi ya ce wanda ake zargin ya rubuta wasika ne da sunan bogi yana ikirarin yin garkuwa da mai shagon da yake tsaro matsawar bai tura masa naira miliyan 1.5 a asusun bankinsa ba. 

Fayemi ya bayyana yadda lamarin ya auku yayin tasa keyarsa tare da wasu matasa biyu inda ya ce sun aikata laifuka daban-daban a sabuwar shekarar nan 

The Punch ta labarta yadda matashin mai shekaru 21 ya yi yunkurin garkuwa da wanda ya ke yi wa aiki yayin amma bai ci nasara ba, don jami’an sun yi ram da shi. 

A cewarsa: “Bayan bincike mai tsawo, an kama matashin a ranar 8 ga watan Janairun 2022. Dama ya na tsare wa mutumin shago ne, amma sai ya shirya wata wasika da suna na daban da lambar asusun banki ya na bukatar naira miliyan 1.5 ko kuma ya sace wanda ya ke yi wa aikin. 

Sai dai sakamakon kokarin yara na, an yi gaggawar nemo shi. Ya yi amfani da wani suna, lambar asusun banki da kuma wata lambar waya na daban don ya yi damfara. Daga nan mu ka binciko lambar wayar sannan mu ka kama shi. Za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike.” 

Kamar yadda ya ce: “Ban so yin garkuwa da shi ba. Na zaci da na yi barazanar zai turo kudin. Na so yin amfani da kudin ne don shagalin kirsimeti, hakan yasa na tura masa wasikar da kuma lambar asusun bankin kuma bai kai ga tura min naira miliyan 1.5 din ba aka kama ni.” 

Har ila yau, an kama wani Ayodeji Fanas mai shekaru 21 bisa zarginsa da satar N500,000 bayan yin basaja da sunan zai taimaka wa wani wurin sayar masa da abin hawa da kuma wani Daniel Emmanuel wanda ake zargin ya sace wasu karafa. 

Source: Legit.ng 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN