Buhari ya dage wajen samar da burtali ga Fulani domin samar da zaman lafiya



Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada kudirin gwamnatinsa na dawo da hanyoyin kiwon shanu a matsayin hanyar magance rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Mista Buhari ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels da aka watsa a ranar Laraba 5 ga watan Janairu, Premium Times ta rahoto. 

Ya ce ya tattauna da ministan noma domin dawo da hanyoyin burtali da aka yi a jamhuriya ta farko musamman a Arewacin Najeriya.

Yan Najeriya da dama sun soki wannan manufar, inda suka ce maimakon haka a sanya makiyaya su yi kiwon shanunsu a wuraren kiwo kebabbu. 

Daruruwan mutane ne ake kashewa duk shekara a fadin Najeriya a tashin hankalin da ke tsakanin makiyaya da manoma. 

A tattaunawarsa, shugaba Buhari ya yi batutuwa da dama da suka shafi kasar nan, musamman ta fuskar yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. 

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN