Rundunar mafarauta ta kasa reshen jihar Kebbi tare da jami'an tsaro sun bankado wani kamfani na kasar waje da ke tafiyar da kasuwanci tare da matasa a yanayi da ya haifar da shakku kan ingancin tafiyar kasuwancin.
Kwamandan rundunar mafarauta ta kasa National Hunters Council NHC reshe jihar Kebbi, Malam Musa Rambo, ya sanar wa manema labarai yayin gudanar da aiki ranar Talata 25 ga watan Janairu.
Ya nuna shakku kan yadda kampanin mai suna Quest International, ke gudanar da kasuwancinsa. Ya ce kampanin kan nemi matasa su biya N500,000 kudin Najeriya. Daga bisani akan rubanya masu kudin a kasuwanci da kampanin ke gudanarwa bisa bayanai da ya samo.
Wannan yana zuwa ne dai dai lokacin da jama'ar jihar Kebbi ke murmurewa daga radadin damfara da wasu kampuna masu ikirarin irin wannan kasuwanci suka jefa su.
Shafin Jaridar isyaku.com ya gano cewa kampanin na da ofishinsa a Unguwar Bayan filin sukuwa. Kuma nan ma'aikatan kampanin ke zaune wanda ke da rinjayen adadin matasa.
Kazalika isyaku.com ya gano cewa mafi yawan wadanda suka zuba kudinsu ga kampanin har N500,000 basu fara shan romon amfanin kudinsu ba duk da lokaci mai tsawo da aka dauka.
Yanzu haka jami'an tsaro na gudanar da bincike kan lamarin Kamfanin da tarin matasa da tuni makwabtan wajen da kampanin ya kama a Unguwar Bayan filin sukuwa ke ma kallon barazana sakamakon wasu dabi'u da matasan da ke kwana a cikin kampanin ke nunawa.
Ku biyo mu domin karin bayani daga jami'an tsaro kan lamarin....
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka