Ƴan vigilante sun kama matasa su na feɗe doki domin siyar da naman ga al'umma a Kano



Rundunar Vigilante, reshen unguwar Kundila sun cafke wasu samari da su ka yanka wani doki a Jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa an kama samarin ne su uku yayin da su ke feɗe dokin a cikin wani aji a  Makarantar Ƴar Kasuwa Firamare da ke Kundila, Ƙaramar Hukumar Tarauni a jiya Litinin.

Ibrahim Muhammad, Mataimakin Shugaban Vigilante na Kundila, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar sa wasu ƴan unguwar ne da su ka ga yaran shine su ka kawowa ofishin nasu rahoto, inda ya ƙara da cewa jami'an su ba su yi wata-wata ba su ka garzaya wajen.

Da isar jami'an wajen, a cewar Muhammad, sai kuwa su ka iske yaran na feɗe dokin, inda kan ka ce kwabo sun cafke su dukka ukun.

Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa samarin sun feɗe dokin ne domin sayar da naman ga al'umma a jihar.

Muhammad ya ce tuni dai su ka tattara bayanan farko kuma za su miƙa samarin ga ƴan sanda domin faɗaɗa bincike, inda a hakan za a gano ko ma sato dokin su ka yi ko akasin haka.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Mazhabobin addinin Musulunci sun bambanta wajen halaccin cin doki.

Amma a Mazhabar Imam Malik, wacce yawanci ita al'ummar Musulmin Nijeriya da ma Afirka su ke bi, cin naman doki Makhruhi ne, ma'ana abu ne maras kyau a addini.

Sai dai kuma wasu Mazhabobin sun riƙe ra'ayin cewa cin doki halal ne.

Daily Nigerian Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN