Kwale-kwale ya kife da Fasinjoji
kimanin 47 ciki har da daliban makarantar Madinatu Islamiyya dake karamar
hukumar Bagwai ta jihar Kano. Daily Trust ta ruwaito cewa kwale-kwalen ya kife
ne a hanyar zuwa Bagwai dake Badau.
Rahoton ya kara da cewa daliban na hanyarsu ta zuwa bikin Maulidi ne don murnar ranan haihuwan Manzon Allah (SAW). Wata majiyar ya bayyana cewa sama da fasinjoji 40 wannan abu ya shafa,
Majiyar, wacce ke asibitin Bagwai ta bayyana cewa kawo yanzu an gani gawawwaki mutum 20 kuma an ajiyesu a dakin ajiye gawawwaki.
An ceto mutum 7, an tabbatar da mutuwar 20 Kakakin hukumar kwana-kwanan jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya ce da misalin karfe 9:15 na dare an tura jami'ai kai dauki, Daily Trust ta jiyo. Ya tabbatar da labarin cewa an gano gawawwaki 20. Ya yi karin bayanin cewa kwale-kwalen na dauke da mutum 47
.
Yace: "A yanzu da muke magana jami'an kai dauki sun gano gawawwaki 20 kuma sun an tsinci mutum 7 da rai." Mummunan hatsarin mota ya laƙume rayukan mutum 15 a Jigawa Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Jigawa ta ce a kalla mutane 15 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar.
Mai magana da yawun yan sandan jihar, Lawan Shiisu, a ranar Litinin a garin Dutse ya ce hatsarin ya faru ne a hanyar Achlafiya zuwa Karnaya, The Nation ta ruwaito.
ASP Shiisu ya ce motoci biyu ne hatsarin ya ritsa da su misalin karfe 5 na yamma a karamar hukumar Yan Kwashi na jihar. Ya ce: "Motoccin biyu sun hadu ne gaba da gaba, sun yi karon ne yayin da daya daga cikinsu ya ke kokarin kaucewa rami a titin.
Source: Legit
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI