Gwamnan arewa ya mayar wa Turji kakkausar martani kan takardar neman sulhu, duba kalamai masu dumi


Gwamna Bello Masari na jihar Katsina ya yi fatali da maganar zaman sulhu da yan bindigan, waɗan da suka addabi jiharsa da sauran jihohin arewa ta yamma.

Masari ya bayyana matsayarsa ne yayin zantawa da kafar watsa labarai ta DW hausa, ranar Asabar.

Premium times ta rahoto cewa gwamnan ya maida martani ga wasikar dake yawo ta neman zaman sulhu, wanda gawurtaccen ɗan bindiga. Bello Turji, ya aike wa gwamnati. 

Gwamna Masari, wanda a baya gwamnatinsa ta rungumi tattaunawar sulhu, yace ba sauran tattaunawar sulhu tsakaninsu da yan bindiga. 

Duk da babu adireshin sa a wasikar, Masari ya bayyana cewa abin da wasikar Turji ta ƙunsa ba gaskiya bane. 

Gwamnan yace: 

"Sulhu da wa? Waye shi da yake neman sulhu ko a tsagaita wuta? Shi babban maƙaryaci ne, bai isa ya faɗa mana yadda za'a zauna lafiya ko sulhu ba." 

"Ƙaje ka samu iyalan waɗan da yan bindiga suka kashe, ku nemi sulhu da su, kuga yadda zata kaya. Kuma har da saka wasu sharuɗɗa, waye shi da zai kafa mana sharuɗɗa?" 

"Shi ke neman sulhu amma har yana da bakin kafa wasu sharudda da za'a cika." 

Tawagar Turji na ɗaya daga cikin kungiyoyin yan ta'adda da suka addabi yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa ta tsakiya. 

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN