Sokoto: Bayan budurwa ta sha duka da tabarya har da kariya kan zargin rashin yin Sallah da sauransu, duba abin da ya faru


Matashiyar yarinya mai shekaru 17 wacce kishiyar mahifiyar ta kusa halakawa a jihar Sokoto za ta samu adalcin da ya dace ta hannun matar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, mariya Tambuwal. 

Uwargidan gwamnan jihar, Mariya Tambuwal, ta umarci kwamishinan shari'a na jihar da ya bincike lamarin tare da gurfanar da duk wanda ke da hannu a ciki. 

Matashiyar yarinyar, diyar tsohon Comptroller na hukumar kwastam kuma Ajiyan Kabi, Alhaji Abdullahi Argungun ce. 

21st century chronicles ta ruwaito cewa, kishiyar mahaifiyar Hafsat ta yi mata dukan kawo wuka da tabarya kan zarginta da sata da kuma rashin sallah tare da sauran laifuka. 

Sakamakon mugun dukan, yarinyar ta kakkarye tare da samun miyagun raunika, 21st Century Chronicles ta ruwaito. 

Sai dai, uwargidan Tambuwal ta yi kira ga antoni janar na jihar Sokoto kuma kwamishinan shari'a, Sulaiman Usman, da ya tsananta bincike kan lamarin tare da gurfanar da dukkan masu hannu a ciki. 

"Ba shakka dole ne iyaye su kula da 'ya'yansu, saboda za su amsa tambayoyi gaban Allah. Hukumomi suna da hakkin yin duk abinda ya dace wurin maganin iyayen da basu dauka nauyinsu.

 "Abinda miyagun suka yi abun kunya ne kuma za a tabbatar da cewa an bi mata hakkinta ko da kuwa mahaifiyar ba ta gidan," Dr Mariya tace. 

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN