Shi ke nan! Farin jinin Buhari ya yi mumunar faduwa bayan hare-haren Yan bindiga a arewa


Farin jinin shugaba Muhammadu Buhari ya yi kasan da bai taba yi ba tun da ya karbi mulki daga hannun Goodluck Jonathan a Mayun 2015. 

Wani bincike da Vanguard for Good Governance Initiative tayi, ya nuna cewa a cikin ‘yan kwanakin nan, karbuwar shugaban kasar ta ragu sosai. 

Daily Reality tace al’umma sun fara cire rai da nuna fushinsu ga gwamnatin APC ta Muhammadu Buhari yake jagoranta ne saboda matsalar rashin tsaro. 

Jaridar ta fitar da rahoto cewa, yardar da aka yi wa shugaban kasar ya ragu daga 58% zuwa 21%. Farin jinin shugaban kasar ya yi kasa ne a watanni biyu. 

Meya faru ake barin jirgin Buhari? Idan aka bi binciken daki-daki, za a ga cewa matsalar rashin tsaro yana cikin dalilan samun canjin. 

Jama’a musamman daga Arewacin Najeriya ba su jin dadin yadda lamarin tsaro ya tabarbare, inda aka sace mutane kusan 400 a watannin bayan nan. 

Wata matsala da ake samu da gwamnatin Muhammadu Buhari ita ce yadda ta gaza shawo kan matsalar tattalin arziki, har yanzu mutane su na kokawa. 

Matsin lamba, hauhawan farashin kaya da tsadar abinci su na cikin abubuwan da suka jawo mutanen da suka yi amanna da Buhari, suke barin jirginsa. 

Tasirin IPOB a Kudu maso gabas Binciken da Vanguard for Good Governance Initiative ta gudanar ya nuna ta’adin da ‘yan kungiyar IPOB suke yi, ya na nakasa tattalin arzikin kudu maso gabas. 

VGGI tace ta gudanar da binciken ne ta hanyar yin waya, aika sakonnin imel, hira da tattaunawa da mutane sama da 150, 000 a watanni uku domin jin ra’ayinsu. 

Abubuwa sun fara sauki a Katsina A yau ne aka ji cewa Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da wasu dattawan jihar sun hadu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock Villa. 

Masari ya yi magana a kan kokarin da suke yi na kawo zaman lafiya a Arewacin Najeriya da kuma wadanda suke je har gida, suka kashe kwamishinansa. 

Source: Legit Nigeria 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN