Mahangar Wasu Kanawa Game Da Hukuncin Kotu Kan Tube Khalifa Sanusi II


Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya ta umarci Antoni-janar na Gwamnatin Kano da ya nemi gafarar tsohon Sarki Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi na II bisa korarsa daga jihar.

A zaman kotun na ranar Talata, Mai Shari’a Anwuli Chikere ta ce korar da Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa tsohon Sarkin Kano daga jihar haramtacciya ne kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Kotun ta umarci Antoni-janar na Gwamnatin Jihar Kano ya wallafa neman gafarar a jaridu biyu na kasar nan.

Kamfanin dillancin labaran na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa Mai Shari’a Chikere tana cewa dokar majalisar sarakunan Kano ta 2019 wadda Gwamna Ganduje ya yi amfani da ita wajen korar tsohon sarkin daga jihar bayan an sauke shi daga kan sarauta ta saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.

A cewar Mai Shari’a Chikere, kundin tsarin mulkin kasa shi ne gaba a kan kowacce doka kuma duk abin da ya ci karo da shi ya haramta.

A shekarar 2020 ce, Gwamnatin Jihar Kano ta sauke Muhammadu Sanusi na II daga kan saraauta saboda zarginsa da nuna rashin biyayya ga dokokin Jihar Kano.

Daga nan ne gwamnatin ta dauke shi a jirgin sama zuwa kauyen Loko da ke Jihar Nasarawa. Sai dai daga bisani an mayar da shi zuwa garin Awe duk dai a cikin Jihar Nasarawan

Amma tsohon sarkin ya kai karar Antoni-janar na Gwamnatin Jihar Kano da babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya da darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kuma Antoni-janar na Nijeriya bisa korarsa daga jihar.

Muhammadu Sanusi na II bai kalubalanci sauke shi daga kan mulki ba, amma ya nemi kotun ta bayar da umarni a sake shi daga tsarewar da aka yi masa a wancan lokacin da kuma dawo masa da ‘yancinsa na kasancewarsa Dan’adam.

Hakazalika, kotu ta hana wadanda ya kai kara tsangwamarsa da kuma keta hakkinsa na Dan’adam.

Alkalin kotun tarayyar ta nemi Gwamnatin Ganduje da wasu daga cikin mutanen da tsohon sarkin ya kai kara su biya Muhammadu Sanusi na II diyyar naira miliyan 10 bisa korarsa daga Jihar Kano.

Wani dan kasuwa mai kuma shugaban Rukunin kamfanin Mai Sallah Tedtile, Alhaji Murtala Mai Sallah ya bayyana cewa hukuncin kotun zai zama kariya ga mutuncin sarakunan gargajiya.

Ya ce, “Mun ji dadi kwarai da gaske da jin hukuncin da kotu ta zartar kan cin zarafin da aka yi wa Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II”.

Alhaji Murtala ya bayyana hakan ne ga Jaridar LEADERSHIP HAUSA a lokacin da yake nuna farin cikinsa bisa wannan umarni na kotu.

Ya ci gaba da cewa, “Mun jima muna fadin cewa kaso mafi rinjaye na matsalolin kasar nan rashin adalcin kotuna ne, saboda haka matukar za a bai wa kotuna dama, babu shakka za a samu adalci a cikin gudanar da harkokin shari’a.

“Wannan mataki da alkali ya dauka ya zama wata kariya ga mutuncin sarakunan da aka sauke, wanda zai hana ci gaba da cin zarafin duk wani sarki da aka sauke daga mukaminsa.”

Ya kara da cewa duk da gwamna na da iko ko damar cire basarake, amma daga yanzu za a daina cin zarafin duk sarkin da aka cire. Ya ce sarakunan gargajiya su ne suka fi kusa da al’umma kuma su ne ke dora al’umma kan tafarkin daidaito da samar da duk wata maslaha a tsakanin mutane.

Da yake bayyana nasa ra’ayin, Malam Ahmed Mai Riga wanda tsohon direba ne, ya bayyana cewa lallai sai an yi hattara wajen aiwatar da wannan umarni da kotu ta bayar, domin a cewarsa, sarakuna biyu a gari daya kowanne na da nasa mabiyan, sannan kuma a irin wannan lokacin musamman ganin yadda ake kallon siyasa ta taka muhimmiyar rawa wajen sauke guda cikin sarakunan da ake magana.

Shi kuwa Malam Abubakar Ladan mai kaji cewa ya yi dole a karfafa harkar tsaro wajen aiwatar da wannan hukunci, domin ka da garin neman gira a rasa ido baki daya, Kano rijiyace gaba dubu shigarta sai dan asali.
Ya ce, “Muna ci gaba da nazari kan hukuncin kotu na biyan Sarki Muhammad Sunusi diyya daga wajen Gwamnatin Kano.”

Gwamantin Jihar Kano ta ce tana nazari a kan hukuncin da  babbar kotu da ke Abuja ta yanke kan biyan tsohon Sarki Kano Muhammadu Sanusi na II diyyar naira miliyon 10 tare da neman gafararsa bisa korarsa daga jihar.

Kwamishinan shari’a na Kano, Barista Musa Lawan ya shaida wa manema labarai cewa sai bayan gwamnati ta yi nazari kan hukuncin kotun sannan za ta san mataki na gaba da za ta dauka.

“Mun sa lauyoyinmu su nemi kundin shari’ar domin mu yi nazari mu san ko za mu daukaka kara ko a’a”. In ji shi.

Rahotun Leadership Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN