Duba ababe 4 da kasurgumin dan bindiga Bello Turji ya nema a wasikarsa ta neman sulhu


Sanannen ɗan bindigan nan da ya addabi wasu yankuna jihar Zamfara, Bello Turji, ya nemi a yi zaman sulhu domin kawo karshen kashe-kashe a yankunan jihar. 

A wasikar da ya aike wa shugaban Buhari, gwamna Matawalle, da Sarkin Shinkafi, Turji, ya sha alwashin aje makamansa bisa wasu sharuɗɗa da ya gindaya. 

A rahoton Aminiya Hausa ta samu kwafin wasikar mai shafi uku, ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Disamba. 

1. Gwamnati ta soke kungiyar yan sa'kai A cewarsa matukar gwamnati ta rushe ƙungiyar yan sa'kai to da izinin Allah duk wani kashe-kashe da yan bindiga ke yi ya zo ƙarshe. Haka nan kuma yace dole sai an cire ƙabilanci da ake nuna musu (wato fulani) a koma ƙasa ɗaya dunƙulalliyar kamar yadda take a baya. 

2. Zaman sulhu da sarakuna da Malamai Ƙazalika a wasikar sa, Turji, ya nemi masarautar Shinkafi ta shirya musu zama da sarakunan ƙasar nan da kuma manyan malamai domin tattaunawar adalci. Ya yi alƙawarin matukar aka shirya wannan zama, to zai karbi duk wata bindiga da ake aikata ta'addanci da ita ya miƙa wa hukumomin gwamnatin Najeriya. 

Wani ɓangaren wasikar, yace: "Idan haka ta samu (Zaman Sulhu) to ni Muhammad Bello Turji Kachalla, na yi alƙawarin zan karbi dukkan bindigun da ake aikata ta'addanci da su na miƙa wa gwamnatin Najeriya." 

3. A daina hattarar mu a ko ina Sanannen ɗan bindigan ya ƙara da tabbatarwa sarkin Shinkafi da gwamna Matawalle cewa su ba faɗa da gwamnati suke son yi ba, kuma ba wata ƙungiya suke yunkurin kafawa ba. Ya bayyana cewa cin zarafin da ake wa Fulani yan uwansu a faɗin ƙasar nan da nuna musu bambanci shine ummul aba'isin wannan abubuwan na rashin zaman lafiya. 

4. Muna bukatar ganin Sheikh Gumi Abu na ƙarshe kamar yadda ya rubuta a wasikarsa, Turji yace yayin zaman sulhu suna bukatar a haɗa manyan sarakuna da manyan malaman ƙasar nan baki ɗaya, kuma suna bukatar ganin Sheikh Ahmad Abubakar Gumi. Bugu da ƙari, yace sun san Sheikh Gumi, ya taba zuwa har inda suke ya musu waazi kuma wa'azinsa ya musu amfani, shiyasa suke son zaman lafiya. 

Daga ƙarshe Turji yace wannan ne dalilinsa na rubuta wannan wasiƙa kuma dagaske yake ba da yaudara ba, kamar yadda baya son a yaudare su. 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN