An ja daga: Yan Majalisar tarayya suna kokarin shan gaban Buhari ko ya ki ko ya so da kudirin dokar zabe


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudirin yi wa dokar zabe kwaskwarima Wasu Sanatoci sun nuna hakan ba za ta sabu ba, sun ce dole za su warware matakin da Buhari ya dauka 

Dokar Najeriya ta ba ‘Yan Majalisar tarayya dama su sha gaban shugaban kasa idan suka samu rinjaye 

A ranar Talata, 21 ga watan Disamba, 2021, Sanatoci suka fara yunkurin warware matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka. 

Daily Trust tace ‘yan majalisa su na so ayi wa dokar zabe garambawul bayan shugaban Najeriyar ya ki amincewa da kudirin da zai wajabta zaben ‘yar tinke. 

‘Yan majalisar dattawan sun tado wannan magana ne yayin da suka yi zaman farko a makon nan. Da alamun za su daga hutunsu saboda wannan magana. 

Wasu Sanatoci da-dama sun bijiro da maganar dokar zaben, inda suka bada shawarar cewa ‘yan majalisa su yi amfani da karfinsu, su shigo da wannan doka. 

Sashe na 58 (5) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya ba ‘yan majalisa damar su iya yin watsi da matakin da shugaban kasa ya dauka, su shigo da wata doka. 

Sai dai babu tabbacin cewa masu wannan shiri za su yi nasara domin shugaban kasar ya na tare da kusan duka Sanatocin jam’iyyar APC da ke majalisar dattawa. 

The Guardian tace Sanata George Sekibo ya fara bijiro da wannan magana, yace ya kamata a tattauna a kan batun, kafin a fara maganar kasafin kudin 2022. 

Sanatoci da yawa sun tabbatar da cewa sun fara neman sa hannun abokan aikinsu, domin su iya warware matakin da Mai girma Muhammadu Buhari ya dauka. 

“A doka, mu na da karfin da za mu iya janye matakin da (Muhammadu Buhari) ya dauka. Wannan shi ne abin da sashe na 58 (4 & 5) na tsarin mulki yace.” 

“Mun samu sa hannun Sanatoci 73 daga kowace jam’iyya domin dokar ta samu shiga. - Sanata Sekibo. 

Abba Moro na tare da Sekibo, yace adadin masu goyon bayan hakan sun haura 80. Sanata Matthew Urhoghide yace majalisa ta taba yin haka a lokacin Obasanjo. 

A makon nan ne aka ji Muhammadu Buhari ya ki sa hannu kan sabuwar dokar zaben da majalisa ta amince da ita wadda za ta wajabta yin 'yar tinke wajen fitar da gwani 

Da ake muhawara a kan maganar kudirin zaben, wasu Sanatoci sun soki shugaban kasa Buhari, suka ce hujjojin da ya bada na kin rattaba hannu a kudirin ba su da karfi. 

Source: Legit.ng 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN