An ba hammata iska tsakanin jami'an Hisbah da fusatattun matasa a Kano, duba dalili


Hargitsi ya barke tsakanin jami'an hukumar Hisbah da wasu fusatattun matasa bayan Yan Hisbah sun yi yunkurin kwace barasa da ake zargin ana sayarwa a Unguwar Sabon gari na jihar Kano ranar Talata 14 ga watan Disamba 2021. Shafin isyaku.com ya samo.

Daily Trust ta ruwaito cewa jami'an Hisbah sun yi diran mikiya a wani mashaya da ake kira Ballat Hughes da ke Court road a Sabon gari domin su kwace barasa da suke zargin ana sayarwa wanda wata Mata ke da mallakin wajen. 

Sai dai jami'an sun fuskanci turjiya daga fusatattun matasa a unguwar, lamari da ya kai ga ba hammata iska da ya haifar da tashin hankali. 

Duk da yake an haramta sayarwa tare da kwankwadar barasa a jihar Kano, amma dokar bata faye tasiri ba kwarai a Unguwar Sabon gari da ke da galibin yawan yan kudancin Najeriya da ba Musulmi ba.

Kazalika Jaridar ta ruwaito cewa lamarin ya yi sanadin take mutane da dama yayin gudu don neman mafaka kuma wasu yan iska suka yi amfani da wannan damar suka yi wa masu wucewa a unguwar fashi kuma aka balle wasu shaguna aka yi sata.

A nata rahotu kan lamarin Jaridar sunnewsonline ta ruwaito cewa an raunata mutane da dama har aka kai wasu asibiti. Yayin da jama'a suka kaurace wa titi a unguwa.

Ta ce matasan sun lalata wata motar sintiri na hukumar hisbah.

Ta ce an kama akalla mutum 26 dangane da lamarin.

Kakakin hukumar yansandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce Kwamishinan yansandan jihar Samaila Dikko ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN