Yunwa: Satar tukunyar abinci a kan murhu ya zama ruwan dare a Enugu, Mutan jihar sun koka


Mutan jihar Enugu na kuka kan yadda satar tukunyar abinci; miya, shinka da wake a kan murhu ya zama ruwan dare a unguwanninsu.

Binciken jaridar Leadership ya nuna yadda barayi suke satar tukunyar abinci yayinda ake kan girkawa.

A hirarta da wata mazauniya Obiagu, ya bayyana yadda ya nemi tukunyar abincin da yake girkawa ya rasa daga shiga cikin daki daukan abu.

A cewarsa:

"Suna na Mrs Ijeomah. Ni mazauniya Ama Awusa ce a Obiagu. Na daura sanwa kan wuta don yarana su ci abinci da yamma. Miyar ta kusa nuna kawai sai nace bari in kara gishiri sai na shiga daki karo gishiri."

"Ina shiga na ji wani kara amma ban taba tunanin wani zai sace tukunyar miya ba. Inda muke zama babu katanga saboda haka kowa na iya shiga. Fitowa na ke da wuya na nemi tukunyar miya na rasa."

"Ban ji dadi ba saboda da daren nan yarana kwana sukayi cikin yunwa. Da barawon ya tambayeni da na sammasa."

Nima haka ya faru da ni?

Wata matar daban kuma wacce ta bukaci a sakaye sunanta ta bayyana yadda akayi awon gaba da miyarta daga kan murhu.

Tace:

"Talauci fa yanzu yayi tsamari. Ta yaya mutum zai shigo gidana na dauke tukunyar miya ddaga kan murhu. Na ji abinda ke faruwa kenan kwanan nan. Yanzu na daina tashi daga bakin murhu idan ina girki."
An tattaro cewa bayan satan tukunyar sanwa da ake yi, wasu sun fara fasa shagunan mutane sun kwashe kayan masarufi a jihar.

Ana kashe mutane, Shugaba Buhari zai yi bayani gaban Allah inji Tsohon Gwamna, Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan matsalar rashin tsaro.

Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa yace a halin yanzu yankin Arewa maso yamma yana cikin masifa. Bafarawa ya bayyana haka da BBC tayi hira da shi.

Babban ‘dan siyasar ya koka kan halin da mutanen yankin na sa da na shugaban kasa ke ciki. Jaridar Vanguard ta bibiyi hirar da aka yi da Bafarawa jiya.

Source: Legit
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN