Type Here to Get Search Results !

Yar Sarkin Kano: Gara an sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure


Shahida, yar Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi, tace ta gwammace barayi su sace mata N500,000 a maimakon ta bawa mijinta kudin ya kara cikin gara domin auro mata kishiya.

Mahaifiyar 'ya'ya biyun ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamban 2021, yayin da ta ke martani kan wata wallafa da aka yi a shafin Instagram. 

Wallafar ya ce:

"Wannan na mata ne. Kina da N500k, za ka bawa mijin ki a matsayin gudunmawa domin ya kara mata ta biyu ko kuma kin gwammace a sace kudin"

A yayin da ta ke bada amsa, Shahida ta rubuta:

"Ba dai sata kadai bane? Babu wanda za a yi wa rauni ko? Zan samu lada ma idan hakan ya faru, wata kila ma in samu ninkin kudin idan na yi hakuri."

Ma'ana dai Shahida ta gwammace barawo ya sace zunzurutun kudin, N500,000 a maimakon ta bawa mijinta ya kara aure.

Legit

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies