Yanzu-yanzu: Kotu ta kama Maina da laifin handamar N2bn daga kudin fansho


Babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin ta kama tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, Abdulrasheed Maina, da laifin sata da wanke kudin haram zuwa na halas.

A wani hukunci da Okong Abang, alkalin kotun ya yanke, ya ce kotun ta kama Maina da laifin satar kudi sama da biliyan 2 na 'yan fansho "wadanda da yawansu sun rasu kuma basu ci guminsu ba," alkalin yace.

"Na kama Maina da laifin aikata zargi na 2, 6, 9, 3, 7 da na 10," Abang yace.
A wata daya da ya gabata, kotu ta daure Faisal Maina, wanda ta kama shi da laifuka ukun da aka zargesa da su wadanda suka hada da halasta kudin haram har N58.1 miliyan.

Har a halin yanzu, babu rahoton cewa Faisal ya na gidan gyaran hali.

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da Maina a gaban Abang a ranar 25 ga watan Oktoba 2019 da kamfanin Common Input Property and Investment Ltd.

An gurfanar da Maina ne kan laifuka 12 da ake zarginsa da su.

Daga cikin zargin da ake wa Maina akwai yin amfani da kamfaninsa domin boye kudin sata har N2 biliyan kuma ya yi amfani da su wurin siya kadarori a Abuja.

Maina ya musanta aikata wadannan laifukan.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN