Type Here to Get Search Results !

Yanzu yanzu: An kama yan fashi a POS za a kone su da ransu, duba abin da yan sanda suka yi


Wasu barayi guda biyu sun sha dan karen duka bayan sun yi yunkurin yi wa wata yarinya fashi da bindiga a wani POS a garin Ughelli na jihar Delta.

Shafin isyaku.com ya samo cewa yarinyar ta yi nassarar rike wandon daya daga cikin barayin bayan barayin sun yi mata sata suka tsere.

Bayan yarinyar ta rike wandon daya daga cikin barayin daram, ta dinga yin kururuwa na neman taimako.

Sakamakon haka wasu matasa suka kai agaji kuma aka kamasu a Unguwar Onoharigho.

Daga bisani samarin sun yi masu hukuncin daba. Domin dai sun yi wa barayin mugun duka.

Kakakin hukumar yansandan jihar Delta Edafe Bright, ya ce barayin sun kure mutuwa a hannun fusatattun matasa ne sakamakon isowar yansanda a wajen da wuri domin har an yi shirin kone su da ransu a garin na Ughelli. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies