Yan mata bakwai Yan shekaru 10 zuwa 12 sun mutu bayan kwale-kwalen da suke tafiya a ciki ya kife a cikin rafi a kauyen Gamafoi da ke karamar hukumar Kafin Hausa a jihar Jigawa.
Shafin isyaku.com ya samo cewa yaran sun baro garin Gafasa ne a karamar hukumar Kafin Hausa kan hanyarsu ta zuwa kauyen Gasanya a karamar hukumar Auyo domin halartar bikin Mauludi.
Basaraken garin Gamafoi, Malam Adamu Haruna ya gaya wa yansanda faruwar lamarin. Ya ce hatsarin ya faru ne da karfe 3:30 na tsakar ranar Alhamis.
Rubuta ra ayin ka