Yan bindigan Katsina sun koma sadarwa tsakaninsu da wayar oba-oba na 'Walkie Talkie' madadin wayar salula


Yan bindiga masu harkokin su a jihar sun koma amfani da wayar salula mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie, lamarin da ya firgita jama’a da dama.

Premium Times ta bayyana yadda Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa ya ce yanzu ‘yan bindiga sun sauya salo.

Duk da datse kafofin sadarwa da gwamnatin ta yi, ‘yan bindiga sun nemo wani zabin wanda su ke ganin zai zama hanyar sadarwa tsakaninsu.

'Yan bindiga a Katsina sun koma sadarwa tsakaninsu da waya mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie

'Yan bindigan Katsina sun koma sadarwa tsakaninsu da waya mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie. Hoto: Premium Times Source: Facebook

A watan Satumba gwamnatin ta yanke hukunci datse kafofin sadarwa a kananun hukumomi 13 a jihar sakamakon yadda rashin tsaro ya tsananta, PremiumTimes ta ruwaito.

A wata tattaunawa da manema labari su ka yi da sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce ‘yan bindiga su na iyakar kokarin ganin sun kawo cikas ga zaman lafiyan jihar.

A cewarsa:

“Duk da tarin nasarorin da aka samu, wajibi ne a kula da yadda ‘yan bindiga suka zama cikas na farko da su ke addabar jihar Katsina.

“Su na kai farmaki ga masu ababen hawa don yashe musu man fetur sannan har bincike kauyaku su ke yi don samun kayan masarufi.

“Yanzu babban abin tashin hankalin da su ka tsiro da shi shine amfani da wayar salula wacce ta ke amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie.”

Inuwa, wanda shugaban kwamitin tsaro ne a jihar ya ce yanzu haka jami’an tsaro su na iyakar kokarin kamo ‘yan bindigan da ke amfani da wayar salular ta Walkie Talkie din.

An kama ‘yan bindiga 724 daga watan Maris zuwa Satumba

A cewarsa, tsakanin watan Maris da Satumba, an kama mutane 480 da ake zargin ‘yan bindiga ne, ana bincike akan 42 sannan an yanke wa 216 hukunci.

Ya kara da cewa an samu sauki akan hare-haren da ‘yan bindigan su ke kai wa tun bayan gwamnatin ta shinfida dokokin tsaro a jihar.

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN