Yan bindiga sun sace mutane sun bukaci a basu wiwi, kwayoyin kodin, N10m, abinci da ruwan sha a matsayin kudin fansa


Wasu yan bindiga sun sace mutum uku a jihar Ogun suka bukaci a basu N10m , surkin tabar wiwi,  kwalayen kwayoyin kodin, ruwan sha da kuma abinci a matsayin ababen fansa.

An tattaro cewa yan bindigar sun buya ne a wani daji a unguwar Obada-Oko da ke birnin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun kuma suka farmaki mazauna Unguwar ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba.

Rahotanni sun ce yan bindigan sun harbe wani tsohon shugaban makarantar Sakandare mai suna Razaq Lasisi yayin da ya yi kokarin tserewa daga hannunsu.

Sakamakon haka ya tsira da raunukan harsashi kuma ya sami kulawa daga wani Asibiti da ke kusa.

Rahotanni sun ce yan sandan ofishin Obada-Oko sun fuskanci yan bindigan, kuma aka yi musanyar harsashi ta hanyar harbe harbe tsakanin yan sanda da da yan bindigan.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce yan sanda sun kama mutum daya dangane da lamarin.
Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN